AN FASA KWAI!!...MUSHA DARIYA 2018






AN FASA KWAI***
Wani mutum ne yayi sabuwar amarya sai ya dauketa ya kaita wani hotel don suyi honey moon dinsu a chan, watau suci amarcinsu a tsanake inji sa'ad khalifa yakubu (sky) .

suna shiga hotel din sai mutumin ya ajiye amaryar tasa a falo don yaje reception ya biya kudin daki ya kar6o makulli. Zaman amaryar keda wuya sai wata karuwa tazo wurinta ta sameta tace "sannu 'yar-uwa naga waccan macucin mutumin kema ya kawoki nan ne ku kwana (ta nuna mijin) toh kar ki sake ya kwana dake bai biyaki ba (ta dauka itama karuwa ce) kiyi maza ki amshi kudinki tun da farko don guduwa yakeyi baya biya don ni shaida ce saboda munsha kwana dashi baya biyana. kuma ki tambayi kowace karuwa a hotel dinnan kiji don kusan duk ya nemesu suna kwana dashi yana guduwa baya biya. kema don naga baquwa ce baki san halinshi bane har kika biyoshi zaku kwana ya cuceki. gashi da shegen neman karuwan tsiya kamar bunsuru don ni tuni ai na gujeshi kar yasa mun qanjamau don naji ana rade-radin wai yanzu ya kamu da qanjaman don cikakken 'Dan-duniya ne"
*Wai in kece amaryar ya za kiyi tun baku tare ba? za kiyi kasada ne ku kwana sannan ki tabbatar ko kuwa ya ya???



Previous
Next Post »

1 comments:

Write comments

LABARAI MAFI SHAHARA