YAR PSYCHOLOGY (ilimin karantar abinda ke ran mutum)





Barkammu da war haka da fatan muna jin dadin wannan dandalin na musha dariya, yau ma mun sake kawo muku wani Labari me lakabi da "YAR PSYCHOLOGY (ilimin karantar abinda ke ran mutum)" saboda haka bayan karanta wannan post munaso kowa yayi koment a shafinnan. mun gode.

  YAR PSYCHOLOGY (ilimin karantar abinda ke ran mutum)

Wani saurayine a makaranta, ya shiga dakin karatu (library) da shigarsa sai ya hango wata kyakyawar budurwa a gefe zaune ita kadai., kun san halin samari da son hulda da yan mata masu kyau, gogan naka sai ya isa inda take yai mata sallama, sai yace mata na ganki ke kadai zaune, shine naga bai dace kyakkyawar mace kamarki ta zauna cikin kadaici ba. shine nace bari na zo na tayaki hira, kawai sai budurwar cikin daga murya tace



"KA GA MALAM NI BA 'YAR ISKA BA CE DA ZAKA CE IN BIKA DAKINKA IN KWANA KAJE CAN KA NEMI 'YAR ISKA IRINKA"

gaba daya hankalin mutanen dake wurin ya dawo kansu, saurayin yaji kamar kasa ta tsage ya shige ciki don kunya, bayan mintuna kadan sai budurwar tazo inda yake tayi kasa da murya tace masa ina karatun psychology ne na iya karantar abinda ke ran mutum, ko ban tambayeka ba na san kaji kunya da abinda nayi ma, saurayin shima sai ya buda bakinsa da karfi yace 

"KWANA DAYA A DUBU HAMSIN (50000) GASKIYA SUNYI YAWA, HALLA AN FADA MAKI SATA NAKE YI?"



gana daya hankalin mutane wurin ya sake dawowa kansu, wasu suka dinga yi mata dariya suna cewa ashe duk kanwar ja ce, saurayin ya kalleta shima yayi kasa da murya yace mata ina karantun law ne na san hanyoyin kama mutum idan yayi min laifi..


YANXU TSAKANIN BUDURWAR DA SAURAYINAN WA YAFI BURGE KA/KI..SABODA HAKA YI COMMENT DA AMSOSHINKU.
Previous
Next Post »

1 comments:

Write comments
Unknown
AUTHOR
23 December 2021 at 15:06 delete

Gaskiya saurayin nan

Reply
avatar

LABARAI MAFI SHAHARA