*MU KIYAYI HASSADA*





A kwai wasu makwabta guda biyu kuma abokan juna, daya talaka daya attajiri. To, ranan nan sai attajirin ya tashi yin kyauta sai ya nemi shawarar talakan cewa: “Malam Tanko, kyauta nake son yi wa wani talaka, shin ko na saya masa gida ya tashi daga gidan haya, ko na saya masa mota ya dinga neman abinci da ita, wanne kake ganin zai fi?” Sai talakan nan ya ce: “Alhaji, ka san talakawa ba a iya musu, kawai ka ba shi Naira dubu goma ya ja jari.” Jin haka shi kuma attajirin sai ya ce: “Da shawararka zan yi amfani.” Nan take ya zaro Naira dubu 10 ya ba shi, ya ce: “Daman kai ne zan yi wa kyautar ba wani ba!




Previous
Next Post »

LABARAI MAFI SHAHARA