LABARI MAI KAYATARWA



Muje zuwa


Kaitsaye na wuce gida
bayan na dawu daga
gurin AIKI.
.
Zuwana gida keda
wuya sai na iske
MARYAM da FATIMA
zaune a falo kowacce
taci kwalliya suna fira.
Nan take sai naji wani
farin ciki ya lullubeni
saboda yanda naga
kansu a hade kamar ba
kishiya da kishiya ba.
.
Cikin sauri suka tarbeni
tare da yimin sannu da
zuwa ko wacce ta karbi
daya daga cikin ledar
dake han'nuna sannan
suka bini a baya
har'zuwa cikin dakina na
hutawa (TIRAKA)
.
Bayan sun kaini daki sai
suka juya tare
han'nunsu rike da juna.
Hmm gaskiya nayi sa'ar
MATA wannan shine
tunanin da yazo min
acikin zaciyata.
.
Jim kadan
bayan fitarsu sai naga
sun dawo, Daya
tana rike da wani TIRE
wanda ke dauke
da wasu kuloli guda 3
daya kuma na rike da
irin dogon kofin nan na
ruwa da kuma wasu
kananan kofina akai
sai suka ajiye agabana.
.
Bayan sun ajiye sai suka
bude duka kulolin kawai
sai naji wani kamshi na
tashi. Nan take sai
nafara diba ina kaiwa
qasa da hanci. Haka
suka zauna agabana
suka jingina da junansu
suna kallo na nikuwa
saidiban girki nake.


Idan
na shanye ruwan dake
cikin qaramin kofin sai
naga ankara zubawa.
.
Na miqa hannu na kenan
da niyar na dauki kofin
ruwa domin naqara
korawa kawai sai naji
kamar ana buganmin
qafa fir'gigi natashi
kadan ya rage na fado
daga kan dogon bencin
danake kwance.
.
Koda nafarka sai naga
me TALIYA da me
ALALE tsaye akaina
sunzo karbar kudinsu.....
.
Anan'ne natuna cewa
kafin na kwanta saida
nasayi taliyar 50 alale ta
50 nahada.... Hmmm.


Previous
Next Post »

LABARAI MAFI SHAHARA