SAURAYI; Masoyiyata kinsan meyene?
BUDURWA; a'a sai ka faɗa abun ƙaunata.
SAURAYI; yau kam Labari mai dadi na taho
miki dashi.
BUDURWA; yawwa annurin raina! Ina
sauraronka..
SAURAYI; labarin guda 1 ne, amma kuma ya
kasu har kashi 4...
BUDURWA; ashe yau zan sha labari!
SAURAYI; ai kuwa zakiyi dariya kam!
BUDURWA; ALLAH!! Wayyo ni! Daman so
nake na sha dariya sosai.
SAURAYI; to ki nutsu zan fara.
BUDURWA; toh inajinka!
SAURAYI; Labarin wani mutum ne da
matarsa...
BUDURWA; ina ji..
SAURAYI; kashi na 1, wata rana zasuje wani
ƙauye akan babur, sai sukazo wani waje da
hanya ta rabu har gida biyu, matar tace su bi
hanyar hagu, shi kuma mijin yace hanyar
dama zasu bi, matar nan fa ta ƙara dagewa
akan sai dai su bi hanyar da tayi hagu. Sai
mijin ya juyo ya kwasheta da mari tasss!
Yace wa matar: ni ke tuƙin babur ɗin ko
ke??? Haka matar taja bakinta tayi shiru...
BUDURWA; hahahahahahaha! Yayi maganin
ta ai!
SAURAYI; to ga kashi na 2, bayan sun bi
hanyar dama suna cikin tafiya, sai sukaga
mai sayerda ɗanyen kifi, su ka tsaya domin
su saya, ko da su ka saya, sai matarsa tace:
kai! Kyanta kifin nan ayi farfesun sa, sai
mijin yace: a'a, soyawa nakeso ayi. Haba!
Nan fa matarsa ta ɗaga hannu ta kwaɗa
masa mari a fuska, tace: "ni ne mai girkawa
ko kai??"...
BUDURWA; hahahahahahahaha! Wayyo
cikina! Ta rama ba bashi kenan?
SAURAYI; hanzarin me kike? Bari kiji ya zasu
ƙare a gaba mana...
BUDURWA; uhmm! To cigaba.
SAURAYI; kashi na 4, bayan.....
(Sai ta katse shi da hanzari)
BUDURWA; a'a masoyina kashi na 3 dai...
sai saurayin nan ya ɗaga hannu ya dage ya
kwaɗawa budurwarsa mari, yace ma ta: "NI
KE BA DA LABARIN KO KE ???"...
Me zaka ce gameda wannan saurayin???
yi comment da amsar ku.....
EmoticonEmoticon