LABARIN BERAN BIRNI DA BERAN DAJI: MUSHA DARIYA 2018






Wata rana beran birni ya ziyarci abokin sa a daji,Beran daji ya tare shi yace muje kaga gida na da suka isa bakin ramin sa sai yace kaga gida na kenan sai beran birni yace gidan kenan sai yace eh mana ,Ya kawo dankali ya bashi sai yace baya ci.Beran daji yace gobe kazo ka in nuna maka gida na a birni sai yace to,washe gari beran daji ya nufi birni beran birni ya tare shi ya kaishi wani gida mai kyau na siminti beran daji ya saki baki yana kallon kauye suna tafiya beran daji yaga kosai zai dauka sai beran birni ya janye shi yace kada ka taba tarko ne suka wuce zuwa wani dakin abinci mai dadi sun fara ci kenan sai yaji taku taf-taf sai yace mu gudu ga masu gidan nan sai suka gudu.Bayan sun fita sun nufi wani dakin sai suka yi arba da kuliya wato mage suka ranta da gudu da kyar suka sha daga nan beran daji yace shi kan zai koma can jeji gidan sa don kuwa yace TSIYA DA KWANCIYAR RAI YAFI ARZIKI DA TASHIN HANKALI.Haka zalika wannan mulkin da na baya.





Previous
Next Post »

LABARAI MAFI SHAHARA