GWAURO BEJI DADI BA!
Bayan na gama Shiryawa zan fita office sai Amaryata ta fito da shagwaΙa ta rike hannun jakar dake rataye a kafaΙa ta tace "Darling yau a gida zaka zauna kayi min kitso ko" sai na juyo na dubeta tareda dafa kafaΙarta nace " amaryata kiyi hakuri sai na dawo" cikin lallausan murya tace "to My Dear" na tafi har naje bakin kofa sai naji tace " HONEY". Juyowar da zanyi sai tayi min wani kallo mai karya zuciya. Bansan lokacin dana saki jakar dake hannuna ba, nan take nayo kwana, na zauna abakin doguwar kujera nace "zo inyi miki kitson" na ture dan kwalin dake kanta na kama lallausan gashinta ina ja tareda shafawa. Ban ankara ba... Saidai naji saukar Mari,Raassss! na mike a firgice ashe wai mafarki nakeyi, Gemun yayana (Uztaz) da muke maleji a katifa Ιaya na kama inata ja. SADIQ wane irin iskanci ne wannan zaka dinga jamin Gemu ina barci? Yayi ta fada a fusace. Kwana nayi cikin takaici ni ban gama mafarkin ba kuma nasha mari πππGwauranta batayi ba kuje kuyi Aure.
EmoticonEmoticon