INAYI INASO NAGA KOWA YANA YI..



MU SHA DARIYA


INAYI INASO NAGA KOWA
YANA YI..
πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚
Wani mutum ne yaje
wajen cin abinci
(Restaurant). Ya samu
waje ya zauna
sai ya kwalawa mai
restaurant kira da
karfi yace "hado min plate
na N2000
kuma ki hadawa kowa
dake wajen nan
plate na N3000 saboda
idan ina cin
abinci, ina so naga kowa
yana ci". Duk
mutanen dake wajen suka
fara godiya
yayinda mai restaurant ta
zubawa kowa
nasa ta kawo masa.
Bayan mutumin ya gama
cin abinci sai
ya kuma cewa mai abincin
"kawo min
drinks na N500 kuma ki
kaiwa kowa na
N1000 saboda idan ina
shan abu, ina so
naga kowa yana sha". Mai
Restaurant ta
kaiwa kowa kayan shaye-
shaye kala
kala yayinda da mutanen
wajen suka
barke da sowar "Allah ya
kiyaye ka!"
Bayan mutumin ya gama
sai ya cewa
mai Restaurant "kawo min
resit na biya
kudina kuma ki kaiwa
kowa nasa resit
ya biya kudinsa, saboda
idan ina biyan
kudina ina so naga kowa
yana biyan
nasa".
Yanzu haka mutumin yana
kwance a
asibiti saboda dan karen
dukan da aka
lakada masa.


Previous
Next Post »

LABARAI MAFI SHAHARA