ZA A YI SANYI: MU SHA DARIYA 2018



Wani Bazazzage ne ya je wurin budurwarsa, suna cikin hira sai kawai hadari ya taso. Kafin ka ce me, an fara ruwan sama mai karfin gaske. Ganin haka sai baban yarinyar ya fito daga gida, ya ce mata: “Da alamu wannan ruwan ba mai tsagaitawa ba ne, watakila a kwana ana yi. Ki shiga ki gyara masa dakin
baki, da safe sai ya tafi.” Nan da nan ta shiga gida ta fara gyara daki, tana gamawa sai suka fito ba su ga Bazazzage ba. Can sai ga shi nan ya shigo a guje, ya jike jagaf. Sai baban ya tambaye shi cewa: “Daga ina haka?” Sai saurayin ya ce: “Gidanmu na je na dauko bargona saboda na san za a yi sanyi cikin dare.”





Previous
Next Post »

LABARAI MAFI SHAHARA