INA DANDANA GISHIRI: MU SHA DARIYA



Wani Bazazzage ne ya ba matarsa kaza domin ta dafa masa, amma ya ce mata kada
ta ci ko kadan. Bayan ta gama dafawa ta sauke, sai ya dawo gidan amma matar ba
ta kusa. Sai ya bude ya firgi cinya daya, ya shige ban-daki yana ci. Can sai ita ma ta zo
ta bude tukunyar, sai ta fizgi cinya daya, ta shiga ban-daki da nufin ta cinye a boye, sai
ta yi arba da mijinta yana cin nama, sai ta ce masa: “Da ma na kawo maka ne don ka
hada ka cinye!” Shi kuma cikin kunya ya ce mata: “Ina dandanawa ne in ji ko gishiri ya ji.”





Previous
Next Post »

LABARAI MAFI SHAHARA