MOTA KO HANNU ? MU SHA DARIYA 2018


Wasu mutane ne su biyu suna fada, daya ya fi dayan karfi. An raba su amma marar karfin ya ki hakura, sai mutane suka ce a rabu da su. Can da mai karfin nan ya yi masa wani wawan naushi, sai ga shi a kasa sumamme. Aka kai shi asibiti, bai san inda yake ba. Can sai ya farfado, ya ga likita a kansa, ya ce: “Likita, ina fatan dai an kama direban motar?” Likita ya ce: “Ai ba hatsarin mota ka yi ba, hannun abokin fadanka ne!”




Previous
Next Post »

LABARAI MAFI SHAHARA