GODIYAR ANGO: MU SHA DARIYA 2018




Wani ango ne ana walimar bikinsa a gaban ’yan uwa da abokan arziki, bayan an kammala sai aka ce ya tashi ya yi jawabin godiya. ANGO: Godiya ga Malam Hashimu dillalin gidaje, wanda ya ba mu aron gidan da za mu zauna kafin mu samu na haya. Ba zana taba mantawa da Hajiya Tasallah Mai Adashi ba, wadda ta ba ni daukar farko don in kai kudin auren. Godiya ga Asabe Dillaliya, wadda ta ba mu bashin atamfofi da shaddodi da muka saka a lefe. Allah Ya saka wa kanwata Basariyya, da taimakonta ne na fita

kunya, inda ta ba mu aron akwatunan lefenta muka saka kayan a ciki, bisa yarjejeniyar mayarwa bayan an gama biki da mako 2. Allah Ya bar zumunci, Ya ba mu ikon cika alkwurran da muka dauka. Ba zan manta Atiku Mai Wanki Da Guga ba, da ya ba ni aron kaya domin in saka a wannan rana. Mun gode.




Previous
Next Post »

LABARAI MAFI SHAHARA