SAURO DA DANSA: MUSHA DARIYA 2018



Wani sauro ne ya fara koya wa dansa tashi, har ya fara kwarewa. Rannan sai uban ya ce masa: “Ya kamata yau ka tashi kai kadai, domin in ga kwarewarka.” dan saurayin sauron nan ya bude fiffikensa ya tashi sama, ya yi shawagi. Bayan ya dawo, ya sauka, sai uban ya tambaye shi cewa: “Shin ya ka ji lokacin da ka tashi?” Cikin farin ciki
saurayin sauron ya gaya wa babansa cewa: “Wato abin da ya fi burge ni, shi ne irin yadda na ga duk inda na wuce mutane na yi mini tafi.”
Uban ya kalle shi ya yi
murmushi ya ce: “ Yaro, ai ba tafi suke maka ba, kashe ka suke so su yi.




Previous
Next Post »

LABARAI MAFI SHAHARA