A YI RIGE-RIGEN TABA KAN MAI SHAYI: MU SHA DARIYA



Wani mai suna Iro mai shayi ne ba ya dawowa gida sai misalin karfe daya na dare. Wata rana yana dawowa sai ya ji ana ta gardama a wani lungu. Ya labe don ganin masu gardama a wannan dare sai ya ga mutum uku ne. daya daga cikinsu ya ce na fi ku sauri, sai sauran biyun suka ce a’a. Sai ya ce to a yi
rige-rigen zuwa bangon duniya. Can ya ji shiru kamar minti uku sai ya ji an ce, ni ne na daya, dayan ya ce ni ne na biyu, sai dayan ya ce, ni ne ya kamata in yi na farko amma saboda tuntuben da na yi da dutsen Uhudu ne ya sa na yi na karshe. Iro Maishayi na labe kwatsam sai ya ji an ce to a yi rige-rigen taba kan mai shayi! Sai kawai ya saki zawo a wandonsa






Previous
Next Post »

LABARAI MAFI SHAHARA