Wata amarya ce bayan daren amarci da ita da angon ta da sassafe ta samo mai baro ta dauko TV tasa ta dauko RADIO tasa ta dauko DVD player tasa ta ce ma yaro ya kai gidan iyayenta. Yaro ya tattara kaya ridi ridi sai gidan su yaba maman ta.
Da yaro ya kai sako sai maman tayi mamaki "ace yariya daga tarewa sai ki kwaso kayan mijin ki ki kawo min" ta aika aka kira ta tace "kekoo SAUDE wannan kayan fa" sai tace "Ai jiyane cikin dare mutumina har kirana Anti yake kuma yace ya bani TV anjima kadan ya kara cewa ya bani RADIO anjima kadan ya kuma cewa ya bani DVD yace harya rasa mema zai kara mini yakara da cewar duk wani abinda na gani in inaso in dauka shiyasa nace bari na kawo muku kuma ku dan more rayuwa kadan". Sai uwar tace " ke don ubanki zo ki kwashi kayan nan ki mayar gidan mijinki. Baban ki sau shida yana bani gidan nan."
EmoticonEmoticon