UP NEPA: MU SHA DARIYA



Wani dan Najeriya ne ya je Ingila ya yi laifi ’yan sanda suka bi shi za su kama shi sai ya shiga wani gidan rawa. Suka rasa yadda za su yi su kama shi. Ashe wani daga cikin ’yan sandan ya taba zama a Najeriya, sai ya ce, β€œKun san yadda za ku yi?” Saura suka ce β€œA’a.” Ya ce, β€œA kashe wutar lantarkin gidan rawar.” Sai aka kashe. Bayan kamar minti uku ya ce a kunna, ana kunnawa sai wannan dan Najeriya ya ce,
β€œUp NEPA!” Sai dan sandan nan ya ce, β€œGa shi can, ku kama shi.





EmoticonEmoticon

:)
:(
=(
^_^
:D
=D
=)D
|o|
@@,
;)
:-bd
:-d
:p
:ng

LABARAI MAFI SHAHARA