Wani mutum ne matarsa ke da mage, kullum ta dame su da barna. Wata rana sai ya dauke ta, ya yi tafiya mai nisa da ita cikin daji da motarsa. Ya aje motar, ya dauki magen ya yi tafiya mai nisa da ita cikin dajin nan, ya jefar da ita. Ya kama hanyar dawowa sai ya yi makuwa, ya rasa inda ya aje motar.
Tun safe yake tafiya har La’asar bai kai ga inda ya aje motar ba, sai ya buga wa matarsa waya, ya sanar da ita halin da yake ciki. Matarsa ta ce: “Ai kuwa bayan tafiyarka da awa biyu sai ga magen ta dawo gida.” Shi kuwa sai ya kara rudewa, ya ce wa matar: “Ba magen waya mu yi magana da ita.
EmoticonEmoticon