WANI YARO 1.: MU SHA DARIYA 2018



Wani yaro ne kullum da dare sai ya lallava dakin kakarsa ya satar mata kudi a cikin akwati. Idan ta ce wa ya daukar mata kudi sai ya yi ta rantse-rantsen karya, cewa ba shi ba ne. Wannan sata da ake yi mata tana damun ta, rannan sai ta samo katuwar kunama, ta sanya a cikin akwatin nan, ta yi kamar tana barci. Gogan naka ya yi sallama ya ji shiru, sai ya danna hannunsa cikin akwatin da niyyar satar kudi kamar yadda ya saba. Kunama kuwa ta harbe shi. Ya kwala kara, ya ce: “Wayyo Allah, kunama ta harbe ni a akwati!” Kakarsa ta fashe da dariya, ta ce: “Yau na kama 6arawona.”




Previous
Next Post »

LABARAI MAFI SHAHARA