SATAR AKUYAR TSOHUWA: MUSHA DARIYA 2018



Wani 6arawo ne yaje sata gidan wata tsohuwa. Bayan ya yi sa'a ya saci akuyar ya kai kasuwa ya sayar naira dubu shida, sai ya laluba jakar sa domin ya hada kudin da na aljihunsa, ashe ya yi rashin sa'a ya zubar da naira dubu ashirin a gidan tsohuwa.
Fitowar tsohuwa ke da wuya sai ta ga ba akuya amma ga daurin kudi a aje kusa da tirken akuya. Tsohuwa ta dauka ta godewa Allah.
Ba jimawa kawai sai ga 6arawon ya dawo gidan sai ya tarar da tsohuwa zaune tana kirga kudi, sai 6arawo ya yi qarfin halin gaisheta, ta kuma amsa mishi. Sai 6arawo ya ce "wallahi Inna akuyar ma dubu shida aka siyar da ita". Sai tsohuwa ta ce "eh haka sha'anin kasuwa yake, yau riba gobe faduwa




Previous
Next Post »

LABARAI MAFI SHAHARA