Wai wata amarya ce da ta kwana uku da zuwa gidan mijinta, sai ga wani yaro ya yi mata sallama da safe bayan mijinta ya fita daga gidan. Yaron yana rike da leda baka, ya mika mata. Ko da ta duba sai ta ga dakwalen kaji ne guda uku, yankakku kuma gyararru. βMijinki ne ya ce na kawo miki.β Inji yaron. Bayan ta koma cikin gida ta fara gyaran tukunya domin dafa kajin, sai ga yaron nan ya sake dawowa, ya ce mata: βMaigida ya ce ki dauko janareto za a kai wurin sabis.β Nan take ta amince ta ba shi.
Can da yammaci bayan maigida ya dawo, amarya ta tarbe shi da manya-manyan kaji, amma da yake ya ga banza ce, sai bai ma tambayi yadda aka yi ba. Ya fara cin kaza yana sharar santi yana ta saka mata albarka. Abinka da kasa ta Najeriya, kawai sai aka dauke wuta. Ko da angon ya zabura domin kunna janareto, sai ya tarar babu shi. Da ya tambayi amarya: βShin ina janareto yake?β Sai ta ce masa: βAi wanda ka aiko ya kawo kajin nan, shi ne ya zo ya ce ka ce a bayar da shi za a kai wurin sabis!β
EmoticonEmoticon